ABNA24 : Bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce; babu wani dalili ko wata doka ta duniya da ta halasta wa Amurka satar danyen man fetur na wata kasa a duniya, amma kuma duk da hakan tana yin fashin danyen man fetur na Syria a yankunan da wasu ‘yan bindiga da take marawa baya suke mamaye da su.
Bayanin ya ce duk kasar da za ta aikata irin wannan mummunan aiki a duniya, ba ta da hurumin da za ta buda baki har soki wata kasa kan saba ka’idoji da dokoki na duniya, kuma hakan ya kara tabbatar da manufar manyan kasashe kan haifar da rikici a kasar Syria, inda a halin yanzu ta bayyana cewa manufar ita ce wawushe arzikin da Allah ya huwace wa kasar.
Wani kamfanin gwamnatin kasar Amurka ya rattaba hannu tare da kungiyar ‘yan bindiga ta Kurdawa da ke dauke da makamai a arewacin Syria wadda Amurka ke mara mata baya, inda kamfanin na Amurka zai gudanar da ayyukan hakar danyen mai na kasar ta Syria tsakaninsa da ‘yan bindigar, yayin da shi kuma sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Mike Pompeo ya ce sun jima suna jiran wannan lokaci.
342/